Bambanci tsaknin Email da Gmail
Menene Email? kuma menene Gmail ?
Wannan tambayace wacce dadama suke neman sanin
wadannan abubuwa guda biyu, saudayawa zakaji mutane in aka tambayesu kanada
Email ne se yacemaka sede Gmail hhhhhh ok!
To menene
Email?
Email hanyace ta turawa da karbar saqo ta yanar gizi
(internet) tayadda saqonnin suna qunshene bisa nau’in yaren computer (0s &
1s) zeros and ones kuma kan nau’in ASCII tex. “zamu sanardaku menene
ASCII codes nangaba insha Allah cikin rubuce rubecenmu”.
Idan muka lura ashe Email hanyar miqawa da karbene
kawai ta yanar gizo. Sannan E tana
nufin Electronic, mail kuma yana nufin Message se suka hadu sukabada Email wato saqqonnin na nau’in wutan
lantarki (Digital); kuma itace hanyar datafi shahara a duniyar yau wajen aika
saqonni cikin sauri dakuma sauki. Tsarin email nayanzu anyishine kan abuda suke
fadi “RFC 5322”(Request For Comments) yanazuwa a tsarin kameda amsa kaitsaye a
nau’in abunda suke kira IMF(Internet
Message Format) a matakin standardized ASCII-base saboda exchange tsakani
na’urori masu kwakwalwa. Mafiya yawan saqonni sukan tafine kan POP (Post Office
Protocol) zamuzo mugayamuku manene Protocol a harkar internet amma atakice protocol shine dan tsakiya me sadarwa
tsakanin user (wato me neman bayanai) dakuma inda aka ajiyesu (Server) dan kasaukesu kan computerka Dafatan
munfahimci menene Email ?.
To manene Gmail
?
Gmail
masarrafce da kamfanin Google ta samar domin aikawa, da karba dakuma ajiyewa na
saqonni masu biyowa ta hanyar yanr gizo masu tafiya a nau’in wutan lantarki.
Kunga ashe Gmail application ne wato akwatine da Google ta kirkira domin ajiyewa
da aikewa da saqonnin Emails (saqqonnin na nau’in wutan lantarki (Digital
messages)).
Sahawara ko hikimar kirkirar wannan akwati na email
messages tasamune agurin makirkirin Google me suna Paul Buchheit a 1990s ta
yannda yafara kirkiro akwatin mesuna Hotmail
kafin Gmail yazama available a gurin kowa afadin duniya ashekara ta 2004.
Sannan dafrko sungina wannan manhajace don ma’aikatan Google kadai dagabaya
kuma google tafahimci tasirin dazeyiwa al’umma da ita kanta haryakai Google
takirkiro kari irnsu Google+, Google drive, Hangouts, You Tube, Google Calender
ds.
Agefe guda Gmail yazama cigari wanda mafiya yawan
mutane sukafi amfanidashi sama da sauran takwarorinsa har nima Ismail Muhammad
inada nawa akwatin domin karbar saqoni shine ismaeela829@gmail.com
hakama akwai na masarrafata wato masarrafa1@gmail.com
.
Akwai sauran applications irin wannnan wanda wasu
kamfanoni suka kirkira kamarsu Yahoo mail, Outlook, Rediffmail, webmail ds.
Damin sanin yadda zaka mallaki naka ko ince bude
naka Gmail din dakanka ta wayar hannunka harma kabudewa wasu cikin sauqi ka
kalli gajeren video da nayi a wannan link : https://youtu.be/B3nyi2TjtgA
.
Munatafe da kananu damanyan shirye-shirye domin ku
muna kuma fatan zakuciga da bibiyarmu dakuma bamu hadin kai dama shawarwari don
cigaban al’uamrmu ta Arewa da wayewarta cikin harshen Hausa dan kowa ya amfana
mukuma zaka awaye kan duk abubwan cigaba nawannan zamani. Kubayyana mana
ra’ayinku aqasa can wajen comment. Ku
kasance da shafukanmu na Masarrafa
Institute of Technology
Ismail Muhammad.