Yadda zaku bude Email ta wayoyin hannunku
Barka dazuwa shafinmu maisuna Masarrafa Institute of technology . Ayau muna tafe da darasi mai matukar muhimmanci wanda dayawa yanacimusu tuwo a kwarya wato Yadda zaka bude emailta wayan hannunka basekaje wajen kowaba kkuma yazauna awayarka kacigaba da amfani dashi kubiyoni ahankali mataki mataki don sanin yadda zaka kirkiramma kanka Email harma kabudewa wani ta wayarka ko ta wayarsa. Dayawa awannan zamani akwatin email yazama mafi muhimmancin wajen ajiya dakuma tura saqo cikin sirri dakuma sauri kuma kyauta. Domin sanin menene Email danna nan Email.
Step 1: Idan kadauki wayarka farko katabbatar ka bude datar wayanka sannan sai kashiga menu nawayarka sannan se kashiga setting nawayarka setting zakaga jeren giyar zabi (options) seka sauka qasa zuwaga inda aka rubuta Accounts sekadanna zakaga accounts dakunan dakabude irinsu Google Accounts (Email), Facebook, Whatsapp, in kana dasu awayarka; se kazo karshen su inda akayi alamar Plus + zakaga anrubuta +Add account sekadanna zebudemaka daki irin wannan; to anan gurin kulura zakuga hotuna masu alamar masakin sako (envelope) an rubbuta Exchange, aqasa dashi kuma akwai alama ta G an rubuta Google to kawai kataba alamar Google din zaibudemaka sabon shafi, idan wayarka da security makullan tsaro ko thumbprint to zatabukaci kasanyasu don ta tabbatar kaine dakaknka idan kasany tabude kaitsaye zata kaika zuwa inda zaka bude Email account, zata tambayeka zakaiyi sign in ne ko zakayi adding account ?
Sekatafi qasa zakaga an rubuta create account se katabashi zakaga karamin windo yabude yacemaka For myself, akasakuma anrubuta To manage my business;
to idan kanaka zaka budewa sekadanna for myself inkuwa wani zaka budewa sekazabi to manage my business zekaika wajen dazaka saka sunannka nafarko da nabiyu sekadanna Next zekaika zuwa gaba wani rami dazece Phone number (sabida yatabbatar kai mutumne )
sekasa lambar dazaka bude da’iata kuma katabbatar tana taredakai koda bata cikin wayar dakake aikin da’ata sekadanna Next Google zasu turu makullan tabbatarwa verification codes guda shida kan lamabar dakasa abaya sekaje kaduba cikin akwatin saqo nawayarka wato (Massage inbox) zakaga Google sekabude sakon zakaga wasu lambobi shide misali G- 509378 to su zaka saka cikin ramin tabbatarwa.
Dazarar kasanya lambobin daidai kadanna Next zai budemaka inda zaka sanya jinsinka (Gender),ran haihuwarka (date of birht) inkagama kadanna
Next seyakaika inda zaka zabi Email adreshinka misalai nawa shine ismaeela829@gmail.com to kaima/kema sai kizabi sunan dayamaka/ki sai ajinginashida @gmai.com missali : suna11@gamil.com indan babu wanda yarigaka wannan suna sai Googgle sukarba inkuwa wani yarigaka zasu cemaka the name is already taken wato anrigada anzabi wannan laqabi saikachanja kokuma google zatabaka shigensu insunmaka sai kazaba. Daganan anzo kusan qarshe inkatura google zasu amince sai suturomaka da tabbaci zakuma sunemi katabbatar da abunda kayi shin kaine ? sai kadanna mus I am in sannan kadanna OK !.
Wanana shine hanya maisauqi wajen qiqirar Email Accouunt tawayar hannunku Android base kaje munci kudinkaba, kuma tawannan hanaya zaka iya budewa wasu kaima imma kyauta kokuma subiyaka qila kasamu hanyar samun kudi kaima tahanyar moriyar ilimi . domin kallon wannan bayani a aikace kuziyarci shafinmu na YouTube https://youtu.be/B3nyi2TjtgA sanan inkunje kudaure kudanna mana Like,da Subscribe da Qararrawa kuma kuyi share sannan kucigaba da bibiyarmu domin samun muhimman bayanai taciki wannan kafa mai albarka.
Albishirinku Jama’a Masarrafa IT munatafe da darrusa masu amfanarwa musamman azamanance kuma musamman tabagaren ilimin sarrafa na’ura mai kwakwalwa (Computer) dakuma wayoyin hannu. Kuma abindazai iya birgeku shine duk bayananmu manayine da harcen Hausa domin jama’armu na Arewa kowa ya amfana.
Subscribe by Email
Follow Updates Articles from This Blog via Email
1 Comments
good
Reply Delete