Sarkin garin Biu na jihar Borno, Mai martaba Umar Mustapha Aliyu, ya rasu a daren Litinin kamar yadda iyalansa suka tabbatar.
Sarki Umar Mustapha ya rasu yana da shekara 80 bayan fama da rashin lafiya, sai dai babu cikakken bayani kan irin cutar da ta yi ajalinsa.
Wani rahoto da Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta wallafa ya ce a yau Talata ake saran yi masa jana'iza a fadar Biu da ke jihar Bornon.
Rahotan ya kuma ce kwamishinan yaɗa labarai da na al'adu, Babakura Abba-Jato ya tabbatar da mutuwar, kuma da misalin karfe 2 na rana ya ce za a yi jana'izarsa.
Allah yajiqan sarki yagafartamasa.
Subscribe by Email
Follow Updates Articles from This Blog via Email
No Comments