INTERNET & NETWORK
Menene Internet?
Internet (Yanar Gizo ) : ita yanar gizo zamu iya cewa farfajiyace da take
hada gamayya/ miliyoyin na’urori masu kwakwalwa (millions of computers) dake
saduwa da juna wajen musayar bayanai ta hanyar gamuwarsu kan wani layi abunda
ake kira Network. Zamu iya fahimtar
cewa shi Internet gonace mai fadi komuce sararine da Allah ya halitta wanda
babu wanda ya mallakeshi; kadauka cewa anguwa/wani garine wanda duk wanda
yariga zuwa yagyarashi seyazama shine me unguwa sekaga dukwanda yazo yanason
yazauna se ya tanbabayi izini ko yasayi fili ko
yazauna haya; to haka internet yake duk wanda yagyarashi ya kwashi guri
yazama mai unguwa.
Mudauka irinsu Google, Yahoo, Host
Gator/(clouding companies) da sauran masu riqe da bayanai (server computers) to
mudauka sune masu unguwa, sune suka debi fegi a sama (Internet) suka kyara
/suka tanadi wani sashi domin amfanin kansu da wasunsu seyazam kai kuma da
kakeso kaima kasamu wani yanki na wucin gadi/haya se kabiya masu unguwa iya
zangon dakakeso kazauna; misali kasayi data
–GB/MB weekly/monthly (ma’ana datar sub din satine ko na watane ?) to kaga yazama kamar kasayi
filin haya idan yaqare sekasake biya wannan shine karamin misali !
Dukda kaima zaka iya mallakar wani sahse
na internet idan ka tanadi kayan mallaka.
Wannan shine taqaitaccen ma’anar internet wato gurine
dake hada dubunnai ko miliyoyin na’urori (collection of thousand computers) dasuke
iya Magana da juna sukumuma raba bayanai atsakaninsu adai dai lokacinda kowanne
acikinsu take awani duri daban. Misali yanzu kana gida ammma kakamo tawa
kwamfutar kana karanta bayanai alhalin nidakai ko tawa da taka kwamfutar basa
tare; sannan abunda ke hadasu shi ake kira NETWORK!
Menene
Network ?
Network mahada : shidai wannan abu
da’ake kira Network wato me hadawa wani abune komuce wani sanadine (titi
ne)dake hada na’ura daga biyu zauwa sama wanda zebasu dama su gaana da juna
shiyasa kakeji idan me kiran waya yasamu damuwar kira sekajiyace babu network
/network problem! To gamuwar wadannan layuyyuka su sukabada abinda kae kira
internet.
Menene
Internet?
Sannan kuma abunda ke bada dama ake isa
zuwa ga bayanai da’ake nema shine Protocol
wato (me iso a faada) kamar yadda kabiyo titi (network) se ka’iso gidan (Internet),
to kafin kasamu shiga sai kanemi memaka iso jagora (protocol) zuwa cikin gidan
(internet). Shi wannan protocol din zamumuku jawabinsa nangaba insha allahu
amma atakaice shine ake kira Hypertext
Transfer Protocol (http) wanda ko dayaushe zakaga kana sashi a rariyar liqau
(browser) naka, saboda isa wajen bayanan dakake nema a internet afadin duniya
shiyasa kake rubuta World Wide Web
(www).
Wannan yasa idan zakanemi bayanai a
internet se karubuta http://www.-------.com.
kokuma .com .net .org .club .edu ds.
Misali kubiyomu ta shafinmu akan
internet (yanargizo) ta hanyar danna
https://www.masarrafa.blogspot.com
idan kuma akwai tsaro (security) zakaga
anrubuta http(s) .
kubiyomu cikin karatuttukanmu don karin sanin
menene (https dakuma www.)
dafatan zamujiku ra’ayoyinku ta sashen Tsokaci (Comment).
Akwai
nau'o'i biyu na hanyar sadarwa ta kwamfuta, wato:
a.
Gidan Yanki na
Yanki (LAN):
Wannan
cibiyar sadarwa tana amfani da igiyoyi don haɗa na’urori tare.
b.
Wide Area Network (WAN):
Irin wannan cibiyar yanar sadarwa tana nufin cibiyar sadarwa wanda aka yada a fadin duniya , yanki, kamar birane ko ƙasashe.
WAN
yana amfani da layi, satellites ko microwaves zuwa haɗa na’uroori tare.
Siffar
ko tsarin cibiyar sadarwa Network Topology
Nau'in
Network (Network Topology)
Abubuwan
dabarun cibiyar sadarwa da muke da su a yau sune:
a.
Bus Topology:
Wannan
cibiyar sadarwar ne inda aka yi amfani da guda ɗaya na USB don samar da ɗayan
ƙarshen na cibiyar sadarwa zuwa ɗayan kuma tare da na'urorin sadarwa
daban-daban da alaka da kebul a wuri daban. Dukansu ƙare na
Ana
gyara igiyoyi tare da maɓallin waya na musamman.
a.
Star Topology:
Wannan
cibiyar sadarwa ce inda duk igiyoyi ke gudana daga na’urori zuwa a babban wuri
inda duk aka haɗa su ta hanyar na'urar da aka kira HUB.
Sadarwa
yana sauri saboda akwai hanyar kai tsaye daga
mai
kula da tsakiya a kowane ƙananan (kumburi).
Karku manta zaku iya kwafan wannan link
dakuma yadashi domin karawa juna ilimi musamman mutanen Arewa;
https://www.masarrafa.blogspot.com
muna kuma
fatan zaku yada (share) na wannan
rubutun damaa sauran rubututtukanmu.
By
Ismail Muhammad.
Subscribe by Email
Follow Updates Articles from This Blog via Email
No Comments